Isa ga babban shafi
Kamaru

An kashe 'yan sanda a yankin 'yan aware

Wasu jami'an tsaro a garin Buea na Kamaru
Wasu jami'an tsaro a garin Buea na Kamaru STRINGER / AFP

Akalla jami’an 'yan sanda biyu aka hallaka a Jamhuriyar Kamaru a ranar Litinin bayan wani hari da aka kaddamar mu su a birnin Buea da ke yammacin kasar .

Talla

Sai dai wata majiyar asibiti ta shaida cewa, jami’an ‘yan sanda biyar ne aka kashe da kuma farar hula guda.

Wannan dai na kara haifar da fargaba game da kazancewar rikici tsakanin jami’an tsaro da ‘yan awaren da ke dauke da makamai a fafutukarsu ta ganin yankinsu mai amfani da Turancin Ingilishi ya samu ‘yanci daga kasar.

Bayanai na cewa, a karon farko kenan da ake kai hari a birnin Buea da ya kasance cibiyar yakin neman ballewar ‘yan awaren.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.