Isa ga babban shafi
Senegal

Kotu a Senegal na ci gaba da tsare wasu yan siyasa

Khalifa Sall daya daga cikin yan siyasa da ake tsare da su aSenegal.
Khalifa Sall daya daga cikin yan siyasa da ake tsare da su aSenegal. RFI/Guillaume Thibault

Wasu Lauyoyin yan adawar kasar Senegal da ake zargi da laifin cin hanci da rashawa sun zargi gwamnatin kasar da amfani da kotuna domin hana wadanda suke karewa tsayawa takarar zaben shekara mai zuwa.

Talla

Gwamnatin kasar ta gurfanar da Karim Wade, dan tsohon shugaban kasa Abdoulaye Wade tare da Khalifa Sall, Magajin garin Dakar da laifin karkata akalar dukiyar jama’a.

Ousseynou Fall, daya daga cikin lauyoyin ya ce hukuncin da kotunan suka yankewa yan adawar siyasa ce kawai.

Da jimawa a kasar ta Senegal yan siyasa dake adawa da gwamnatin Macky Sall sukan fuskanci barazana a cewar kungiyoyi da ma yan siyasa a wannan kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.