Isa ga babban shafi
Najeriya

Taron makiyaya da manoma a Abuja

Yankunan da ake fuskantar rikicin manoma da makiyaya
Yankunan da ake fuskantar rikicin manoma da makiyaya DeAgostini/Getty Images

Shugabanin Kungiyoyin manoma da makiyaya a Najeriya sun gudanar da wani taro na fahimtar juna a Abuja, inda suke cewa babu gaskiya kan rahotan da ya mamaye kasar cewar rikici tsakanin su ne ke haifar da kashe kashe.

Talla

Da farkon rikicin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce idan da bai yi karatu ba shima da ya kasance cikin rikicin Makiyaya da Manoma da ya addabi kasar tare da gurgunta al'amuran tsaro a wasu yankunan.

Muhammadu Buhari da ya ziyarci wasu yankunan kasar kama daga jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriyar ya kuma bukaci iyaye da su jajirce wajen ganin sun sanya yaransu a makarantu.

A cewarsa galibin rikice-rikicen na faruwa ne sanadiyyar rashin ilimi daga bangarorin biyu masu fada da juna.

Bayan taron nasu, shugabannin sun bayyana cewar hukumomin tsaro su sake bincike kan wadannan kashe kashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.