Isa ga babban shafi
Senegal

Kotun Senegal ta daure jagoran ta'addanci shekaru 20 a yari

Tun a watan Aprilun da ya gabata aka fara sauraron shari'ar wadda aka kammala yanke hukuncinbta a yau Alhamis.
Tun a watan Aprilun da ya gabata aka fara sauraron shari'ar wadda aka kammala yanke hukuncinbta a yau Alhamis. RFI/Guillaume Thibault

Wata kotu a birnin Dakar da ke Senegal ta daure jagoran kungiyar mayakan jihadi, Mukhtar Diokhane shekaru 20 tare da ayyukan wahala a gidan yari, abin da ake kallo a matsayin daya daga cikin manyan shara’u da ke da nasaba da ayyukan ta’addanci a kasar.

Talla

Shari'ar wadda aka faro ta tun a ranar 9 ga watan Aprilun da ya gabata kan akalla mutane 29 da ake zargi da taimakawa ayyukan ta'addanci a kasar inda shari'ar ta yau kotun ta wanke mutane 14 daga cikinsu.

Baya ga jagoran tafiyar Makhtar Diokhane wanda kotu ta yankewa hukuncin daurin shekaru 20, akwai kuma limamin tafiyar wanda dama ke tsare a hannun hukuma inda aka yanke masa hukuncin dauri na wata daya bayan samusa da laifin mallakar bindiga marar lasisi.

A shekara ta 2015 ne jami’an tsaro a Senegal suka kame wasu daga cikin mutanen da aka gabatarwa alkali, yayinda jami’an tsaron Jamhuriyar Nijar suka yi nasarar kama Makhtar Diokhane bayan samu sa da laifin kashe kudaden jabu a kasar, suka kuma mika shi zuwa Sanegal.

Bayan sauran tuhume-tuhumen da kotu ta samu Makhtar da hannu dumu-dumi a cikinsu akwai kuma zargin hannunsa a wasu ayyukan ta'addanci a yankin arewa maso gabashin Najeriya mai fama da rikicin kungiyar Boko Haram ko da dai ya musanta zargin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.