Isa ga babban shafi
Turai

EU ta fuskanci sabon kalubale kan shirin rage kwararar bakin-haure

Wasu bakin-haure a babban birnin kasar Libya, Tripoli, wadanda jami'an kasar ta Libya suka ceto daga hallaka a teku.
Wasu bakin-haure a babban birnin kasar Libya, Tripoli, wadanda jami'an kasar ta Libya suka ceto daga hallaka a teku. REUTERS/Ismail Zitouny

Shirin magance matsalar kwarar bakin-haure zuwa turai ya fuskanci koma baya, sakamakon shawarar da Italiya ta yanke na kin karbar ‘yan ci ranin da aka ceto daga hallaka a teku.

Talla

Cikin wasikar da ya aikewa kungiyar kasashen turai EU, ministan harkokin waje na Italiya Enzo Moavero, ya ce kasar ba za ta amince da komawa kasa daya tilo da ake jibge bakin-hauren da aka ceto daga teku ba.

A gefe guda kuma kasar Libya ta yi watsi da tayin kungiyar tarayyar turai na gina sansanonin ajiye ‘yan ci ranin da ke niyyar ketarawa Turai, a wani shiri na rage yawan wadanda suke kwarara zuwa nahiyar.

Zalika kasashen Masar, Morocco da kuma Tunisia sun ki amincewa da shirin gina sansanonin bakin-hauren, bayan da kungiyar ta EU ta yi musu tayi.

Kasar Albania ma dai ta bi sawun matakin kin amincewa da tayin gina sansanonin ajiye bakin-hauren da kungiyar EU ta gabatar mata, inda Fira Ministan kasar Edi Rama, ya bayyana sansanonin a matsayin sharar da kowace kasa ke gudu daga gareta.

Mafi akasarin bakin-haure ko ‘yan ci ranin da ke hankoron keterawa nahiyar turai na fitowa ne daga nahiyar Afrika, yankin gabas ta tsakiya da kuma kudancin nahiyar Asiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.