Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Sojin Najeriya sun fatattaki 'yan Boko Haram a Yobe

Kasashen Chadi da Najeriya da Nijar da Kamaru na cigaba da fuskantar hare haren kungiyar book haram.
Kasashen Chadi da Najeriya da Nijar da Kamaru na cigaba da fuskantar hare haren kungiyar book haram. Reuters

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarun ta da ke aiki a Jihar Yobe sun yi nasarar murkushe wani hari da mayakan kungiyar boko haram suka kai musu a Sasawa da ke karamar hukumar Babbangida ta jihar.

Talla

Kakakin rundunar sojin, Janar Texas Chukwu ya ce sun yi nasarar kashe mayakan da dama wandada suka yi yunkuri kai hari kasuwa domin kwashe kayan abinci.

Jami’in ya ce wasu daga cikin dakarun su sun samu raunuka a artabun da suka yi.

Nasarar ta Sojin Najeriya na zuwa a dai dai lokacin da mayakan na Boko Haram suka hallaka akalla mutane 18 ta hanyar yanka su da wuka baya ga sace wasu mata 10 a makociyar Najeriyar Chadi.

Wata majiyar soji ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar, an kai harin ne da misalign karfe 9 na dare a kauyen Daboua, da ke kusa da iyakar Jamhuriyar Nijar.

Kasashen Chadi da Najeriya da Nijar da Kamaru na cigaba da fuskantar hare haren kungiyar book haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.