Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Farfesa Umar Pate kan bukatar Robert Mugabe na kayar da Jam'iyyarsa a babban zaben kasar

Sauti 03:34
Tsohon shugaban kasa Robert Mugabe ya bukaci masu kada kuri’a da su kori Jam’iyyar ZANU PF daga karagar mulki a ganawar da yayi da manema labarai.
Tsohon shugaban kasa Robert Mugabe ya bukaci masu kada kuri’a da su kori Jam’iyyar ZANU PF daga karagar mulki a ganawar da yayi da manema labarai. REUTERS/Siphiwe Sibeko

Yau 'Yan kasar Zimbabwe ke gudanar da zaben shugaban kasa, irin sa na farko bayan kawo karshen mulkin shugaba Robert Mugabe, wanda ya kwashe shekaru kusan 30 a karagar mulki.Shugaba Emmerson Mnangagwa mai shekaru 75 daga Jam’iyyar ZANU PF ta tsohon shugaban kasa Mugabe na fafatawa ne da Nelson Chamisa mai shekaru 40 a Jam’iyyar MDC ta marigayi Morgan Tsvangirai.Tsohon shugaban kasa Robert Mugabe ya bukaci masu kada kuri’a da su kori Jam’iyyar ZANU PF daga karagar mulki a ganawar da yayi da manema labarai.Mun tattauna da Prof Umar Pate na Jami’ar Bayero kuma ga tsokacin da yayi kan zaben.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.