Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojoji sun kama kwamandan Boko Haram na 96 da suke farauta

Wasu daga cikin mayakan Boko Haram da sojin Najeriya da suka kama, a watan Yuli na shekarar 2018, wadanda suka taka rawa wajen sace daliban makarantar Chibok a shekarar 2014.
Wasu daga cikin mayakan Boko Haram da sojin Najeriya da suka kama, a watan Yuli na shekarar 2018, wadanda suka taka rawa wajen sace daliban makarantar Chibok a shekarar 2014. REUTERS/Ahmed Kingimi

Rundnar sojin Najeriya ta sanar da damke wani kwamandan kungiyar Boko Haram da ta shafe lokaci mai tsawo tana neman sa ruwa a jallo.

Talla

Kakakin rundunar sojin Najeriya Birgediya Janar Texas Chukwu ya ce dakarun Najeriya sun kame Maje Lawan ne a garin Banki, da ke jihar Borno, wanda shi ne na 96 a jerin kwamadojin kungiyar Boko Haram da suke farauta.

Birgediya janar Chukuwu ya ce Maje Lawan ya shiga hannunsu ne bayan da ya yi nasarar kshiga cikin wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke garin na banki.

A wani labarin kuma kakakin sojin na Najeriya, ya ce sun samu nasarar hallaka wasu mayakan Boko Haram biyu, bayan da suka yi musu kwanton Bauna a kauyen Malari da ke jihar ta Borno, yayinda wasu mayakan da dama suka tsere da raunuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.