Isa ga babban shafi
Chadi

Chadi ta rufe wuraren hakar zinari na arewacin kasar

Janar Oumar Bikimo tareda rakiyar Shugaban kasar Idriss Deby Itno a Djamena
Janar Oumar Bikimo tareda rakiyar Shugaban kasar Idriss Deby Itno a Djamena STR / AFP

Gwamnatin Chadi ta bayar da umurnin rufe dukkanin wuraren hakar zinari da ke yankin arewacin kasar iyaka da Libya, biyo bayan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a garuruwan Miski da Kouri Bougri da ke yankin.

Talla

Ministan tsaron cikin gidan kasar Ahmat Bashir ya bai wa jami’an tsaro umurnin lalata rumfunan da kuma na’urorin da masu hakar ma’adinan ke amfani da su a yankin.

A baya Chadi ta sanar da rufe kan iyakarta da kasar Libya saboda tsaro daga barazanar ‘yan ta’adda dake yin kutse a cikin kasar. Sai dai Chadi ba ta fayyace ‘Yan ta’addar da ta ke nufi ba.

Firaministan Chadi na lokacin ne ya sanar da daukar matakin a jawabin da ya gabatarwa ‘yan kasar ta kafar Radio da Talabijin na gwamnatin.

Firaministan ya ce gwamnatin ta dauki matakin domin barazanar da ta ke fuskanta ta kwararar ‘yan ta’adda daga kan iya tsallakowa cikin Chadi daga kudancin Libya.

Chadi ta rufe iyakar ne a yankin Tibesti yanki mai cinkoson jama'a ‘yan kabilar tubawa da ke rayuwa a kan iyaka da Libya.

Kasar Chadi na kan gaba a yaki da ta’addanci a Afrika inda Sojojinta ke samun goyon bayan Amurka da Faransa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.