Isa ga babban shafi
Ethiopia

Jami'an tsaro sun kame mutane 800 da ke son tayar da rikici a Habasha

Babu dai tabbacin ko mutanen 800 na da alaka da sabon rikicin da ya yi kokarin barkewa yau a yankin amma rahotanni sun ce tuni aka baza jami'an tsaro don tabbatar da zaman lafiya.
Babu dai tabbacin ko mutanen 800 na da alaka da sabon rikicin da ya yi kokarin barkewa yau a yankin amma rahotanni sun ce tuni aka baza jami'an tsaro don tabbatar da zaman lafiya. REUTERS/Tiksa Negeri/File Photo

Mahukunta a Habasha sun kame akalla mutane 800 da ake zargi da yunkurin tayar da sabon rikici a kasar wadda ba ta jima da farfadowa daga tashe-tashen hankula ba.

Talla

Rahotanni sun ce a makon nan kadai jami’an tsaro sun kame mutane kusan 500 bayan wasu 300 da suka kame a makon jiya wadanda dukkaninsu suka taka muhimmiyar rawa wajen asassa rikici a kasar.

Beyissa Kuma wanda shi ne kakakin gwamnati a yankin na Oromia da ke fama da tashe-tashen hankula, ya ce mutanen 800 na da hannu mamayar matsugunan al’umma da kone muhallan wasu baya ga sanya shingen binciken bag aira babu dalili don tayar da hankula.

Babu dai tabbacin abin da ya haddasa barkewar wani sabon rikicin kabilanci a yankin yau Alhamis amma wasu majiyoyin labarai na nuni da cewa an kai tarin jami’an tsaro don kwantar da hankula.

Matakin kame masu rura wutar rikicin kasar na zuwa a dai dai lokacin da sabon shugaban kasar Ahmed Abiy ke kokarin dai daita al’amura musamman ta fuskar sakin fursunonin siyasa da dawo da alaka tsakanin kasar da makociyarta Habasha dama bunkasa hanyoyin kudaden shigar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.