Isa ga babban shafi
Najeriya

Janar Augustine Agundu ya gargadi matasan dake daukar makamai

Wasu mata a garin  Luggere, na jihar Filato dake tarrayar Najeriya
Wasu mata a garin Luggere, na jihar Filato dake tarrayar Najeriya AFP/Stefan Heunis

Rundunar Sojin dake aikin samar da zaman lafiya ta umurci daukacin mutanen dake zama a wasu yankunan birnin Jos dake Jihar Filato da su zauna cikin gidan su sakamakon wani tashin hankalin da aka samu jiya Lahadi.

Talla

A jawabin da ya yiwa al’ummar Jihar ta kafar rediyo da talabijin, Janar Augustine Agundu ya gargadi matasan dake daukar makamai suna tada hankali da su shiga taitayin su, yayin da yayi kira ga shugabannin jama’a da na addinai da su gargadi matasan su kawo karshen tashin hankalin da ake samu ko kuma su gamu da fushin hukuma.

Rahotanni sun ce an samu arangama da kuma kone kone a wasu sassan birnin Jos, bayan tashin hankalin da aka samu ranar alhamis.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.