Isa ga babban shafi
Kamaru

Boko Haram ta nakasa tattalin arzikin Kamaru

Rikicin 'yan aware da na Boko Haram sun nakasa tattalin arzikin Kamaru a yayin da ake shirin gudanar da zaben shugaban kasa a karshen mako
Rikicin 'yan aware da na Boko Haram sun nakasa tattalin arzikin Kamaru a yayin da ake shirin gudanar da zaben shugaban kasa a karshen mako ALEXIS HUGUET / AFP

Yayin da a karshen wannan mako ake gudanar da zaben shugaban kasar Kamaru, in da shugaba Paul Biya ke fafatawa da wasu ‘yan takara 7, rahotanni sun ce rikicin Boko Haram da kuma ayyukan ‘yan aware sun yi wa yankin arewacin Kamaru illa sosai ta fannin tattalin arziki.

Talla

Alkaluma sun ce mutane sama da miliyan 1 da dubu 200 ke zama a yankin daga cikin sama da miliyan 6 da rabi na masu kada kuri’a a fadin kamaru, yayin da masana'antun da ke yankin suka durkushe.

Kungiyar masana’antun Koko da Kofi ta kasar GICAM, ta ce, yankunan Arewa maso Yamma da Kudu maso Yammaci da ake amfani da harshen Ingilshi, da ke dauke da kashi 20 cikin dari na al’ummar kasar, su ke samar da akasarin Koko, da kuma Kofi ‘yar Arabiya da kasar ke fitar da su kasuwannin ketare.

A cewar GICAM, lardin Kudu maso Yamma kadai na samar da kashi 45 na Koko ga kasar, yayin da lardin Arewa maso Yamma ke samar da kashi 75 cikin dari na Kofi, to sai dai kungiyar ta ce, sakamakon rikicin da ake fama da su a yankunan biyu, ya haifar da koma-baya a ribar da ake samu da kusan kashi 20 cikin dari.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, akalla mutane dubu 246 suka kaurace wa gidajensu yayin da dubu 25 daga cikinsu suka nemi mafaka a Najeriya a Lardin Kudu maso Yamma kadai.

Lardin Arewa mai nisa ma ya samu koma bayan tattalin arziki tun daga shekarar 2014 sakamakon hare-haren Boko Haram, abin da ya tilasta wa mazauna karkara da ke samarwa yankin abinci, tserewa zuwa birane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.