Isa ga babban shafi
Kamaru

An Bude Rumfunan Zaben Shugaban Kasa A Kamaru

Ma'aikatan zabe na kafa kayan zabe a Buea na kasar Kamaru ranar 6 Octoba 2018.
Ma'aikatan zabe na kafa kayan zabe a Buea na kasar Kamaru ranar 6 Octoba 2018. AFP

Yau lahadi ake zaben shugaban kasar Kamaru inda shugaba Paul Biya mai shekaru 85 ke neman wa’adi na bakwai a wani lokaci da ‘yan aware dake yankin da ake Magana da turanci ke kai hare-hare a yankunan su.

Talla

Wakilinmu Mahaman Salissou Hamissou ya aiko mana da rahoton dake cewa jama’a na fitowa don jefa kuriar su muysamman a birnin Yaounde.

Zaben na zuwa ne kwana daya bayan hadewar biyu daga cikin manyan jam’iyun adawa biyu a karon farko.

Shugaban kasar Paul Biya na jefa kuri’arsa a tashan zabe dake Makarantar Bastos dake birnin Yaounde.

A jiya musulmi a birnin Yaounde suka gudanar da addu’oi don rokon Allah ya sa ayi zaben cikin kwanciyar hankali da lumana

An gudanar da adduoin ne karkashin jagorancin limamin masallacin Sheikh Mahaman Saminu.

Yayin da ake shirin zaben kasar Kamaru yau lahadi rahotanni na cewa jiya Asabar ‘yan aware uku aka bindige har lahira a yamutsin da ake samu tsakanin jami’an tsaro da ‘yan aware a yankin da ake Magana da harshe turancin ingilishi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.