Isa ga babban shafi
Najeriya-Buhari

Shugaba Buhari ya hana mutane 50 ficewa daga Najeriya

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari bayan dawowa daga jinya
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari bayan dawowa daga jinya REUTERS/Stringer

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi amfani da kudurin doka na musamman mai lamba 6 domin hana wasu muhimman mutane 50 da ake zargi da rashawa ficewa daga kasar.

Talla

Sanarwar da mai taimaka wa shugaban kasar a game da yada labarai Garba Shehu ya fitar, ta ce wadanda aka dauki matakin hana wa ficewa daga kasar ana zargin su ne da rashawa, kuma kowanne daga cikinsu ya mallaki dukiyar da ta haura naira milyan 50.

A cikin makon da ya gabata ne wata kotun tarayya da ke Abuja ta bayyana kudurin mai lamba 6 da cewa ba inda ya saba wa dokokin Najeriya, hasali ma yana bai wa bangaren shari’a damar yin bincike a game da duk wata dukiya da ake zargin cewa an same ta ne ta rashawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.