Isa ga babban shafi
Uganda

Lokacin mika mulki ga matasan Afrika ya yi-Bobi wine

Robert Kyagulanyi da aka fi sani da Bobi Wine
Robert Kyagulanyi da aka fi sani da Bobi Wine Isaac Kasamani / AFP

Fitaccen mawaki kuma dan Majalisar Dokokin Uganda, Bobi Wine ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da kalubalantar shugaban kasar, Yoweri Museveni da ya bayyana a matsayin mai mulkin kama-karya, yayin da ya ce, lokaci ya yi da ya kamata a bai wa matasa damar rike madafun iko a kasashen Afrika.

Talla

Wine, wanda tsallake rijiya da baya a wani yunkurin salwantar da ransa a Uganda, ya bayyana haka a yayin zantawa ta musamman da wakilin RFI a birnin Nairobi na Kenya.

Mawakin ya ce, lokaci ya yi da ya kamata shugabannin Afrika da suka shafe shekara da shekaru akan karagar mulki da su bai wa matasa damar jan ragama don samar da nagartattun kasashe.

Mawakin ya koka kan yadda shugaba Museveni ke ci gaba da kankamewa kan kujerar mulki duk da cewa shekaru 32 kenan da ya fara jagorancin Uganda, wato tun lokacin da Bobi Wine ke da shekaru hudu da haihuwa.

Wine wanda asalin sunansa Robert Kyagulanyi, ya kuma zargi Museveni da ruguza cibiyoyin gwamnati, in da yake yi wa Majalisar Dokoki da kuma bangaren shari’a hawan-kawara, abin da ya ce, ba za su amince da shi ba kuma za su ci gaba da kalubalantar haka.

Mawakin ya tunatar da RFI lokacin da suka hadu da Museveni a fagen yakin neman zabe, amma aka yi musu dukan tsiya har ta kai ga harbe direbansa har lahira.

“Shugaba Museveni ba ya kaunar shan kaye a zabe, amma kuma yana aikata abubuwan da ke haddasa shan kayi a zabe.” In ji mawakin kuma dan adawa.

Kazalika shugaban ya yi fice wajen bayar da makuden kudade a lokacin zabuka da dama don ganin jam’iyyarsa ta samu yawan kuri’u, amma duk da haka jam’iyyar na shan kashi a wasu mazabu da ke kasar kamar yadda Bobi Wine ya yi karin bayani a hirar da RFI.

“Akwai lokacin da na kayar da jam’iyyrsa da sama da kashi bakwai a mazabata duk da biliyoyin kudade da Museveni ya rabar” In jin Bobi Wine.

Wine ya kara da cewa, shugaban ya yi fice wajen kama ‘yan takara tare da tsare su a jajibirin ranar zabe, abin da ke ba shi damar lashe zabe.

Daga karshe Wine ya bayyana waka a matsayin abun da ya daukaka sunansa a duniya, kuma ya ce, wakar ce ta taka muhimmiyar rawa wajen yakin neman zabensa har ya samu kuri’un cancantar zama dan Majalisa a Uganda.

Mawakin ya yi fice wajen rera wakar fafutukar tabbatar da adalci da ‘yancin fadin albarkacin baki a kasashen Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.