Isa ga babban shafi
Gabon

Gwamnatin Gabon na yiwa al'ummar kasar karya

Ali Bongo Ondimba, shugaban kasar Gabon
Ali Bongo Ondimba, shugaban kasar Gabon REUTERS/Tiksa Negeri

Jam’iyyar adawa a kasar Gabon ta zargi fadar shugaban kasa da yiwa al’ummar kasar karya kan halin da shugaba Ali Bongo ke ciki, bayan ya kwashe kusan makonni uku yana jinya a kasar Saudi Arabia.

Talla

Jam’iyyar National Union tace wasu mutane a fadar shugaban kasar na yiwa jama’a karya, wajen sanar da su gaskiyar halin da shugabaAli Bongo Ondimba nasu ke ciki.

Mai Magana da sunan shugaban Ike Nguoni ya bayyana cewar shugaban na fama da tsananin gajiya ne, amma kuma yana samun sauki, yayin da wasu rahotanni ke cewa Shugaba Ali Bongo ya gamu da bugun zuciya ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.