Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Rikicin Boko Haram ya mayar da mata dubu 54 zawarawa a Borno

Galibi zawarawa da yara marayun da aka kashe iyayensu ko kuma mazajensu a rikicin na Boko Haram yanzu haka na mawuyaciyar rayuwa ba tare da taimako daga ko'ina ba.
Galibi zawarawa da yara marayun da aka kashe iyayensu ko kuma mazajensu a rikicin na Boko Haram yanzu haka na mawuyaciyar rayuwa ba tare da taimako daga ko'ina ba. REUTERS

Gwamnan Jihar Barno da ke Najeriya Kashim Shettima ya bayyana cewar rikicin boko haram ya mayar da mata dubu 54 da dari 9 da 11 sun zama zawarawa saboda kashe mazajen su, yayin da yara 52,311 suka zama marayu.

Talla

Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi fitaccen malamin addinin Islama, Sheik Mufti Menk da ya ziyarce shi a Maiduguri.

Shettima ya shaidawa malamin cewar mayakan boko haram sun lalata kashi 30 na gidajen da ke Jihar da yawan su ya kai 959,453 tare da azuzuwan makarantu 5600, wadanda suka hada da makarantun firamre 512 da Sakandare 512.

Galibi zawarawa da yara marayun da aka kashe iyayensu ko kuma mazajensu a rikicin na Boko Haram yanzu haka na mawuyaciyar rayuwa ba tare da taimako daga ko'ina ba

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.