Isa ga babban shafi
Nijar

Boko Haram na ci gaba da garkuwa da mutane 39 na Ngalewa

Wani yankin yan gudun hijira a jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar
Wani yankin yan gudun hijira a jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar REUTERS/Luc Gnago

A kwana a tashi kwanaki 500 kenan cur, da mayakan Boko Haram suka yi awon gaba da mutane 39 da suka hada da mata da kananan yara a garin Ngalewa da ke jihar Diffa a Jamhriyar Nijar.

Talla

Iyalai da kuma kungiyoyin kare hakkin bil’adama a kasar ta Nijar, sun bayyana damuwarsu dangane da yadda har yanzu mahukuntan kasar suka kasa ceto wadannan mutane.

Rashin ceto mutanen na ci gaba da haifar da fargaba a yankin inda masu fafutukar ganin an ceto su suka shigar da kokensu zuwa hukumomin kasar ta Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.