Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

Masu sanya Ido 200 na kasashen Afrika za su yi aiki a Zaben Congo

A dai dai lokacin da zaben kasar ta Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo ke rage kasa da mako biyu, ana ci gaba da fuskantar rarrabuwar kai tsakanin bangarorin adawa yayinda gwamnatin kasar ta ki amincewa da masu sanya Idanu na Turai.
A dai dai lokacin da zaben kasar ta Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo ke rage kasa da mako biyu, ana ci gaba da fuskantar rarrabuwar kai tsakanin bangarorin adawa yayinda gwamnatin kasar ta ki amincewa da masu sanya Idanu na Turai. © REUTERS

Akalla mutane 200 ne daga kasashen Afrika za su sanya idanu a zaben Jamhuriyyar Demokaradiyyar Congo da zai gudana ranar 23 ga wannan wata na Disamba, bayan da kasar ta ki amincewa da masu sa ido na Tarayyar Turai.Congo dai a karan kan ta ta horar da masu sanya ido na cikin gida fiye da dubu 40, wadanda za su aiki tare da wadanda kasashen Afrika suka turo.

Talla

Wakilin kungiyar kungiyar kasashen Afrika AU da ke Congo, Abdu Abarry, ya ce yanzu haka masu sanya idon 20 sun isar Congo yayinda wasu 80 za su isa kowanne lokaci daga yanzu, baya ga wakilan kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta tsakiya guda 20 daga kasashe 11  da suka kunshi Burundi, Kamaru, Jamhuriyar Congo, Gabon, Rwanda da kuma Tchadi.

A bangare guda shi ma kwamitin bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika ta kudu, ya tura mutane 94 inda 73 daga cikinsu su ka barbazu a jihohin kasar 16 daga cikin 26 da ta ke da su.

Shugaban kasar mai barin gado, Joseph Kabila ya sanar da cewa, gwamnatinsa ta horar da fiye da yan kasa dubu 40, wadanda za su zuba ido a zabubukkan da za su gudana ranar 23 ga wannan wata.

Hukumar zaben Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo CENI ta bayyana cewa akalla mutane miliyan 40 ne za su kada kuri'a a zaben na makon gobe yayinda ta ce za ta yi amfani da na’urorin zabe dubu 100 a rumfunan zabe dubu 80 da kasar ke da su.

Sai dai Tuni kungiyar kasashe masu amfani da harshen Faransanci OIF ta bayyana gano fiye da kashi 16 cikin dari na wadanda za su kada kuri'a a zaben cewa basu da alamar tambarin hannu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.