Isa ga babban shafi
Najeriya-Ta'addanci

Rundunar sojin Najeriya za ta yi jana'izar jami'anta fiye da 100

Ana dai ganin rashin sanar da jana'izar musamman ga manema labarai baya rasa nasaba da zargin da ake na cewa rundunar na boye adadin yawan sojinta da suka mutu a fagen daga.
Ana dai ganin rashin sanar da jana'izar musamman ga manema labarai baya rasa nasaba da zargin da ake na cewa rundunar na boye adadin yawan sojinta da suka mutu a fagen daga. STEFAN HEUNIS / AFP

Rahotanni daga Najeriya na cewa, rundunar Sojin Kasar na shirye-shiryen gudanar da jana’izar fiye da sojoji 100 a gobe juma’a wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar harin mayakan Boko Haram kan runduna ta 157 cikin watan Jiya.

Talla

Wata jaridar kasar The Punch wadda ta zanta da guda cikin matan sojojin da suka mutu a harin na watan jiya, kuma Jaridar Solacebase ta shafin Intanet ta wallafa labarin a yau, ta ruwaito matar sojin na cewa rundunar ta gayyace ta jana’izar amma ba ta son sanar da ita ga jama’a.

A baya dai babban Hafson sojin Najeriyar Janar Yusuf Tukur Burutai ya ce soji 23 ne suka mutu a harin, duk kuwa da ikirarin kungiyar Boko Haram na cewa ta hallaka soji fiye da 100.

Hakan ya sa sashen hausa na Rediyo France International ya yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar sojin Najeriyar Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka amma har zuwa lokacin da muke wallafa wannan labari bai amsa sakon da muka aike masa ba, haka zalika bai waiwayi kiran da muka yi masa ta wayar salula ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.