Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo

Yan siyasa na zargin junan su a gobara da ta kone kayakin zabe

kashi 80% na kayyakin da ya kamata a yi amfani da su a birnin na Kinshasa ne suka kone kurmus.
kashi 80% na kayyakin da ya kamata a yi amfani da su a birnin na Kinshasa ne suka kone kurmus. RFI

Gwamnati da ‘yan hamayya a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo na zargin juna da haddasa gobarar da ta yi sanadiyyar konewar babban rumbun ajiye kayayyakin zabe a birnin Kinshasa fadar gwamnatin kasar.

Talla

Bayanai sun ce kashi 80% na kayyakin da ya kamata a yi amfani da su a birnin na Kinshasa ne suka kone kurmus.

Gwamnati ta ce lura da yadda ‘yan adawa ke nuna rashin amincewa da yin amfani da na’aurar tanttance masu kada kuri’a a lokacin zaben, ga alama tana da masaniya wajen kona rumbun, yayin da ‘yan adawar ke cewa gwamnatin ce ta kitsa lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.