Isa ga babban shafi
Mali

MDD ta zargi mafarautan Dogon da yi wa Fulani kisan kiyashi

Wasu daga cikin mafarautan kabilar Dogon da ke zirga-zirga a tsakanin yankin tsakiyar Mali da arewacin kasar Côte d'Ivoire da ake zarginsu da hallaka mutane 32 a wasu kauyukan kasar ta Mali.
Wasu daga cikin mafarautan kabilar Dogon da ke zirga-zirga a tsakanin yankin tsakiyar Mali da arewacin kasar Côte d'Ivoire da ake zarginsu da hallaka mutane 32 a wasu kauyukan kasar ta Mali. AP

Wani binciken Majalisar Dinkin Duniya ya zargi wasu mafarauta ‘yan kabilar Dogon a Mali da laifin kisan kiyashi a tsakiyar kasar, inda suka kashe Fulani makiyaya 24 a watan Yuni.

Talla

Rahotan da rundunar samar da zaman lafiyar ta MINUSMA ta jagorancin rubutawa, yace an harbe mutanen ne da bindiga mai sarrafa kanta da kuma bindigar farauta.

Minusma ta baiwa gwamnatin Mali shawarar girke karin dakaru a Yankin domin tabbatar da zaman lafiya.

Zuwa yanzu dai an shafe kusan shekaru uku da fuskantar tashin hankali tsakanin Fulani makiyaya da kabilun Bambara da na Dogon mafarauta a yankin Mopti da ke tsakiyar Mali.

Rikicin ya fara ne, bayan da ‘yan kabilar Dogon suka zargi Fulani makiyaya da yi musu barna a gonaki ta hanyar sakin dabbobinsu domin kiwo, yayinda Fulanin suka zarge su da yunkurin tauye musu hakkin samun filayen kiwo da ruwan sha.

A farkon watan Disamba, kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta zargi mayakan sa kai na kabilar Dogon da hallaka Fulani makiyaya akalla 75.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.