Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo-Zabe

Soji 15 sun jikkata a wani sabon hadarin jirgin Jamhuriyar Congo

Wannan ne karo na biyu cikin kasa da kwanaki 5 da Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo ke fuskantar faduwar jirgi.
Wannan ne karo na biyu cikin kasa da kwanaki 5 da Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo ke fuskantar faduwar jirgi. Reuters

Akalla sojoji 15 suka jikkata sakamakon fadowar wani jirgi Fasinja lokacin da ya ke gab da sauka a filin jirgin saman Beni da ke gabashin Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo, kwanaki 3 bayan makamancin hadarin jirgin ya hallaka jami'an zabe 5 a Kinshasa.

Talla

Rahotanni sun ce jirgin na dauke da Fasinja 68 baya ga ma'aikatansa hudu lokacin da abin ya faru wadanda dukkaninsu suka samu raunuka.

A cewar mai magana da yawun ma'aikatar tsaro a filin jirgin na Beni, Captain Make Hazukai, jirgin ya samu matsala ne lokacin da ya ke gab da sauka.

Ko a ranar Alhamis din da ta gabata ma, wani gadarin jirgin sama dauke da jami'an hukumar zaben kasar ta Congo a birnin Kinshasa ya hallaka akalla mutane 6 bayan fadowar jirgi jim kadan bayan tashinsa.

Rahotanni sun ce jirgin ya ajje wasu nau’rori da takardun zabe ne inda kuma ya samu matsalar ta shi matakin da ya haddasa masa hadari tare da hallaka jami'an zaben da ke cikin 6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.