Isa ga babban shafi
Najeriya

Musulman Najeriya sun taya takwarorinsu Kirista murnar Kirsimeti

A cewar Fasto Yohana Buru ta haka ne kadai za a hada kan mabiya addinan biyu baya ga kawo karshen rikicin da su ke fuskanta a tsakaninsu.
A cewar Fasto Yohana Buru ta haka ne kadai za a hada kan mabiya addinan biyu baya ga kawo karshen rikicin da su ke fuskanta a tsakaninsu. NAN

Fiye da mabiya addinin Islama fiye da 500 ne suka ziyarci gidan wani fitaccen Limamin Majami’a a jihar Kadunan Najeriya Fasto Yohana Buru don ta ya takwarorinsu mabiya addinin Kirista murnar zagayowar ranar Kirsimeti da ake alakantawa da haihuwar Annabi Isa.

Talla

Tarin musulman da suka kunshi shugabannin gargajiya da na addini da limaman masallatai da kuma matasa maza da mata har ma da kananan yara wadanda suka fito daga sassan jihar daban-daban, sun isa gidan limamin majami’ar tun da safiyar yau, matakin da ke nuna karuwar dankon alaka tsakanin mabiya addinan biyu.

Yayin ziyarar Fasto Yohana Buru ya jagoranci addu’ar zaman lafiya inda ya ce ta hakan ne za a kara dankon alaka tare da kawo karshen bambancin fahimtar da ke tsakanin mabiya addinan biyu.

A cewar Fasto Yohana Buru lokacin da ya ke karbar bakoncin musulman fiye da 500 ciki har da wadanda suka zo daga kasashen Nijar da Kamaru yana cike da farin cikin ganin lokacin da rikicin addini ke gab da zama tarihi a kasashen.

Shi ma dai Dr Yusuf Nadabo guda cikin jagororin musulmin da suka kai ziyarar ta murnar Kirsimeti, cewa ya yi ta hanyar shigowar kungiyoyin addinan biyu da shugabannin ne za a magance wannan matsala ta rikicin addini.

Dr Yusuf Nadabo wanda tsohon shugaban sashen ilimin kimiyyar sassan jikin dan adam ne na kwalejin kimiyya da Fasaha ta jihar Kadunan, ya ce matukar shugabannin addinai da na al’umma da kuma kungiyoyin fararen hula suka mike tsaye wajen wayar da kan jama’a babu shakka rikicin addini zai zama tarihi a Najeriyar dama makotanta Jamhuriyyar Nijar da Kamaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.