Isa ga babban shafi
Sudan

‘Yan sanda sun yi amfani da harsashi mai kisa kan masu zanga-zanga

Wani sashi na masu zanga-zanga a Khartoum, babban birnin Sudan, yayin kokarin kaucewa hayakai mai sa hawaye da jami'an tsaro ke harba musu.
Wani sashi na masu zanga-zanga a Khartoum, babban birnin Sudan, yayin kokarin kaucewa hayakai mai sa hawaye da jami'an tsaro ke harba musu. REUTERS

Rahotanni daga Sudan sun ce ‘yan sandan kwantar da tarzoma sun yi amfani da harsashi mai kisa wajen kokarin tarwatsa daruruwan masu zanga-zanga, da ke kokarin isa fadar gwamnatin kasar a birnin Khartoum.

Talla

Da fari dai jami’an tsaron sun yi amfani ne da hayaki mai sa hawaye wajen kokarin tarwatsa masu zanga-zangar, amma hakan bai samu ba, saboda sun ci gaba da tunkarar fadar gwamnatin ta hanyar amfani da kyallaye wajen rufe fuskokinsu.

Arrangamar tsakanin masu zanga-zanga da jami’an tsaro wadda ta auku a ranar Talata, ita ce mafi muni, tun bayan soma zanga-zanga da wasu dubban ‘yan kasar suka yi a sassa daban daban kan karin farashin biredi, wadda ta juye zuwa ta kin jinin gwamnati.

Hotunan bidiyo da aka wallafa a kafofin intanet, hadi da rahotanni sun nuna masu zanga-zangar na rera waken neman sauya gwamnati ta hanyar tilastawa shugaban kasar Omar al-Bashir ya yi murabus.

Sai dai yayin da yake yi wa wasu magoya bayansa jawabi a ranar ta Talata, shugaba al-Bashir ya zargi wasu ‘yan kasashen ketare da hannu wajen haddasa zanga-zangar, wadda ta zama mafi girma cikin shekaru da dama a tsawon lokacin da shugaba al-Bashir ya shafe yana mulkin Sudan na shekaru 29.

Alkalumman gwamnati sun ce mutane 12 suka mutu zuwa yanzu, sai dai a nata rahoton kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce masu zanga-zanga 37 ne suka mutu yayin arrangama da jami’an tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.