Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo-Ebola

Shirin rigakafin cutar Ebola ya samu gagarumar nasara

Wasu jami'an lafiya da ke aikin dakile yaduwar cutar Ebola.
Wasu jami'an lafiya da ke aikin dakile yaduwar cutar Ebola. REUTERS/James Giahyue

Ma’aikatar Lafiyar Jamhuriyar Congo, ta ce mutane 502 sun rasa rayukansu, tun bayan sake bullar cutar Ebola a kasar cikin watan Agustan bara.

Talla

Sai dai yayin da yake kain bayani kan halin da kasar ke ciki dangane da bullar cutar, Ministan Lafiya, Ilunga Kalenga, ya ce a karon farko shirin gwamnati da hadin gwiwar hukumomin lafiya na duniya wajen yiwa al’ummar kasar rigakafi, ya samu nasarar kare mutane dubu 76, da 425 daga kamuwa da cutar.

A watan Agustan bara Ebola tasake bulla a arewacin yankin Kivu, da yayi iyaka da kasashen Uganda da Rwanda, karo na 10 kenan kuma cutar na bulla a Jamhuriyar Congo, tun bayan soma gano ta a kasar cikin shekarar 1976.

Hukumar lafiyata duniya WHO, ta ce barkewar cutar a baya bayan nan, da ke haddasa zubda jinni ta kafofin jiki, bayaga zazzabi mai zafin gaske, ita ce annoba ta biyu mafi girma, bayan bullar cutar a kasasshen Saliyo da Liberia a shekarun bayan, inda ta hallaka sama da mutane dubu 11,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.