Isa ga babban shafi
Ivory Coast

Ba zan ce uffam ba kan sakin Gbagbo- Ouattara

Shugaban Cote d'Ivoire Alassane Ouattara
Shugaban Cote d'Ivoire Alassane Ouattara REUTERS/Afolabi Sotunde

Shugaban Cote d’Ivoire Alassane Ouattara ya ki cewa uffam dangane da sakin da Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ta yi wa tsohon shugaban kasar, Laurent Gbagbo.

Talla

Yayin wata hira ta musamman da RFI, shugaba Ouattara ya ce, ba zai ce komai kan wanke Gbagbo daga zargin da ake yi masa ba, amma kuma ya zama wajibi wani ya dauki alhakin kisan da aka yi wa mutane sama da 3,000 da suka mutu sakamakon rikicin siyasar kasar.

Ouattara ya ce, suna ci gaba da gudanar da bincike domin gano wanda ke da hannu wajen tashin hankalin da ya yi sanadiyar hallaka dimbin mutanen.

Dangane da murabus din shugaban Majalisar Dokokin Kasar, Guillame Soro daga mukaminsa kuwa, shugaba Ouattara ya ce, babu matsala a tsakaninsu, sai dai banbancin ra’ayin siyasa.

Rahotanni na cewa, Soro wanda tsohon jagoran ‘yan tawaye ne, na takun-saka da Ouattara kuma akwai yiwuwar tsayawarsa takarar shugaban kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.