Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamna Kashim Shettima ya ketare rijiya da baya

Gwamnan Jahar borno Kashim shetimma a lokacin da ya ke kai ziyara a Baga inda aka kai harin da ya kashe mutane 185 a Jahar Borno Arewacin Najeriya
Gwamnan Jahar borno Kashim shetimma a lokacin da ya ke kai ziyara a Baga inda aka kai harin da ya kashe mutane 185 a Jahar Borno Arewacin Najeriya REUTERS

Rahotanni daga Jihar Barnon Najeriya sun ce wasu yan bindiga da ake zargin mayakan kungiyar boko haram ne sun kai hari kan tawagar Gwamnan Jihar Barno Kashim Shettima inda suka kashe wasu daga cikin yan tawagar sa.

Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa yace mayakan sun yiwa tawagar kwantan bauna ne da misalin karfe 6,30 na yammacin jiya kusa da garin Dikwa.

Kamfanin dillancin labaran Faransa yace cikin tawagar harda dan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar APC,Babagana Umaru,sai dai bayanai sun ce shi da gwamna Shettima babu wanda ya samu rauni.

Bashir Ibrahim Idris ya tuntubi wakilinmu Bilyaminu Yusuf dake Maiduguri kuma ga bayanin da yayi masa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.