Isa ga babban shafi
Najeriya

2019: PDP ta bukaci soke sakamakon zabe a wasu jihohi

Ko a jiya ma dai Jam'iyyar ta PDP ta zargi APC da sayen kuri'u a jihar Kano, jihar da ke jerin wadanda suka fi kawowa jam'iyyar ta APC kuri'a
Ko a jiya ma dai Jam'iyyar ta PDP ta zargi APC da sayen kuri'u a jihar Kano, jihar da ke jerin wadanda suka fi kawowa jam'iyyar ta APC kuri'a AFP

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, ta yi watsi da sakamakon zaben shugabancin kasar da hukumar INEC ta bayyana cewa shugaban kasar mai ci Muhammadu Buhari ne ya lashe zaben wa’adi na biyu.

Talla

Matsayar ta PDP na zuwa ne bayan kiran da ta yi ga hukumar ta INEC da ta dakatar da aikin bayyana sakamakon kuri’un da aka kada a zaben shugabancin kasar, gabannin shelanta nasarar Buhari da ta yi da safiyar ranar Laraba 27 ga watan Fabarairu.

Kakakin jam’iyyar ta PDP Tanimu Turaki, ya bukaci soke sakamakon zabukan shugaban kasa na jihohin Zamfara, Yobe, Nasarawa da kuma Borno.

A cewar jam'iyyar ta PDP akwai tarin kura-kurai a tsarin tantance masu kada kuri'a wanda kuma a yanzu ne suka gano.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.