Isa ga babban shafi
Najeriya-Zabe

'Yan Najeriya na shirin kada kuri'a a zaben Gwamnonin jihohin kasar 29

Akwatin zaben Najeriya
Akwatin zaben Najeriya guardian.ng

Al'ummar Najeriya da ke jihohin kasar 29 daga cikin 36 na shirye-shiryen fita rumfunan zabe a gobe Asabar 9 ga watan Maris don kada kuri'a a zaben gwamnoni da 'yan Majalisun jiha, zaben da ake saran ya samar da sauye-sauye a tsarin siyasar kasar.

Talla

Sai dai a cewar shugaban hukumar zaben Najeriyar mai zaman kanta INEC Farfesa Mahmud Yakubu ya ce baya ga zaben a jihohi 29 da ya kunshi na Gwamnoni da na Majalisun jihohi, za kuma a gudanar da zaben wasu mazabun tarayya a Jihohi 14 da ke fadin kasar.

Acewar Farfesa Yakubu zaben 'Yan Majalisun tarayyar a jihohi 14 ya kunshi kujerun Majalisar Dattijai 7 da na Majalisar wakilai 24 wadanda wasu matsaloli suka hana gudanar da su a watan jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.