Isa ga babban shafi
Nijar

Jami’an tsaron Nijar sun cafke wasu mafarauta yan Najeriya

Daya daga cikin mafarauta a nayihar Afrika
Daya daga cikin mafarauta a nayihar Afrika Getty Images/Robert Ross

Jami’an tsaro a Jamhuriyar Nijar, sun cafke wasu mafarauta ‘yan Najeriya dauke da sassan wasu dabbobin dawa da aka hana farautarsu, kuma ga alama sun kashe dabbobin ne a gandun dajin Park-W da ke daf fa iyakar Nijar, Burkina-Faso da Jamhuriyar Benin.

Talla

Jami’an kare gandun daji a jihar Dosso sun kama sassan dabbobin ne a cikin motoci biyu, da suka hada da hauran giwa, kawunan bauna da na birai, sannan kuma da fatar kasa da wasu macizai da ke karkashin kariyar doka.

Da jimawa hukumomin wadanan kasashe suka sanar da daukar matakan da suka dace domin kawo karshen haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.