Isa ga babban shafi

Kasashen Afrika da guguwa ta afkawa na neman agajin gaggawa - MDD

Wani sashi na birnin Beira da ke kasar Mozambique da ambaliyar ruwa ta mamaye, sakamakon guguwar Idai.
Wani sashi na birnin Beira da ke kasar Mozambique da ambaliyar ruwa ta mamaye, sakamakon guguwar Idai. IFRC/Red Cross/Reuters

Majalisar dinkin duniya ta ce za ta kaddamar da gidauniyar neman tallafi don taimakawa kasashe 3 na kudancin Afrika da iftila’in guguwar ta ‘Idai’ ta afkawa.

Talla

Masu aikin ceto sun kara himma wajen ci gaba da gudanar da aikin ceto a yankunan da guguwar mafi muni ta afkawa cikin fiye da shekaru 10.

Majalisar dinkin duniya ta ce ta samu tallafin dala miliyan 20 daga asusun bada taimakon gaggawa, dan taimakawa wadanda iftila’in ya rutsa da su, a daidai lokacin da rayuwar dubban mutane ke cikin hadari.

Hukumomi sun ce kwanaki biyar bayan da guguwar ta ‘Idai’ ta aukawa kasashen Mozambique, Zimbabwe da Malawi, adadin wadanda suka mutu a Iftila’in ya haura 300, yayin da rayuwar wasu dubban mutane da ke cikin hadari.

Guguwar da ta soma daga mozambique ta bar alummar kasar cikin tashin hankali.

Kakakin kungiyoyin agaji ta kasa da kasa Caroline Haga, ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa suna da karancin lokaci wajen karasa aikin ceton, ganin cewa akwai dubban mutane da suka share tsawon kwanaki 3 makale a kan itatuwa da rumfunan gidaje da ke birnin Beira, suna jiran a kai musu dauki.

Caroline Haga ta ce ko a Talatar da ta gabata an ceto mutane 167 dake makale a rumfuna da itatuwa, zalika sun mayar da hankali kan yara, masu juna biyu da kuma wadanda ke fama da rauni.

Shugaban kasar Mozambique Filipe Nyusi ya ce adadin ‘yan kasarsa da suka mutu a Iftila’in sun haura 202 bayaga kusan dubu 350 wadanda suka jikkata.

Ita kuwa Gwamnatin Zimbabwe ta ce adadin wadanda guguwar da ambaliyar ta shafa a kasarta da suka hallaka ya kai 100, sai dai ana zaton da adadin ya kai 300, yayinda wasu dubu 150 suka rasa muhallansu a dalilin guguwar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.