Isa ga babban shafi
Mozambique

FAO ta kaddamar da gidauniyar tallafawa wadanda ambaliya ta shafa

Wasu mutane akan rufin gidajensu a garin Buzi dake yankin tsakiyar Mozambique sakamakon iftila'in ambaliyar ruwan da ya afka musu. 20 March 2019.
Wasu mutane akan rufin gidajensu a garin Buzi dake yankin tsakiyar Mozambique sakamakon iftila'in ambaliyar ruwan da ya afka musu. 20 March 2019. Photo: Adrien Barbier

Hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya FAO ta kaddamar da gidauniyar neman tara dala miliyan 19 domin tallafawa jama’ar da iftila'in guguwa da ambaliyar ruwa ya shafa a Mozambique, Zimbabwe da Malawi, musamman manoma, masunta da sauran masu ayyukan da suka shafi noma.

Talla

Ifitila’in dai yafi shafar Mozambique, inda kashi 80 na al’ummar kasar suka dogara akan noma.

Rahoton hukumar samar da abincin yace tallafin na dala miliyan 19 zai isa yin amfani ne kawai nagajeren lokacin da bai wuce watanni 3 ba, la’akari da cewa ambaliya da guguwar da suka afkawa Mozambique sun yi sanadin lalacewar yankunan da ke samar da akalla kasha 1 bisa 4 na amfanin gonar da ‘yan kasar suka dogara a kai.

A wani labarin kuma, jami’an lafiya a Mozambique sun ce ana ci gaba da samun karuwar masu fama da cutar kwalara a garin Beira da ambaliyar ruwa ta afkawa a dalilin mahaukaciyar guguwa.

Jami’an sun ce a yanzu haka adadin wadanda suka kamu da cutar ta Kwalara ya karu daga 138 zuwa 271.

A ranar 14 ga watan nan guguwar Idai dauke da ruwan sama ta afkawa garin Beira da ke Mozambique da wasu sassan Zimbabwe da Malawi, inda ta hallaka sama da mutane 700 a kasashen na kudancin Afrika bayan haddasa ambaliyar ruwa.

Har yanzu dai jami’an agaji basa iya zuwa wasu yankuna masu yawa da ambaliyar ruwan ta yanke hanyoyinsu a kasashen Mozambique da Zimbabwe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.