Isa ga babban shafi
Afrika ta kudu

Al'ummar Afrika ta kudu na jiran sakamakon kuri'un da suka kada

Sakamakon da ya fara fitowa dai na nuna jam'iyyar shugaba Ramaphosa ta ANC ce ke da gagarumin rinjaye
Sakamakon da ya fara fitowa dai na nuna jam'iyyar shugaba Ramaphosa ta ANC ce ke da gagarumin rinjaye LOUAI BESHARA / AFP

'Yan Kasar Afirka ta kudu na dakon sakamakon zaben shugaban kasa da ya gudana jiya Laraba, wanda ake saran Jam’iyyar ANC duk da matsalolin da take fuskanta ta samu nasara.

Talla

Ana saran sakamakon zaben ya nuna yadda Yan kasar goyan bayan sabon shugaban su, Cyril Ramaphosa wanda ya gaji Jacob Zuma da aka tilastawa sauka daga mukaminsa.

Tuni dai sakamakon da ya fara fitowa ke nuna jam'iyyar ta ANC na samun gagarumin rinjaye.

Cikin kalaman shugaba Cyril Ramphosa bayan kada kuri'a a zaben ya bayyana cewa ''Damar da zamu samu daga wannan zabe, zai bada damar gaggauta bunkasa tattalin arzikin mu ta hada kan kowanne bangare, domin magance matsalolin da suka addabi talakawan da ke tsakanin mu''.

Shugaba Ramaphosa ya ci gaba da cewa ''Damar da za mu samu anan, ita ce ta gaggauta samar da yi wa jama’a aiki kuma inata fadin cewar, bana bukatar bada Karin uzuri, ina bukatar mu ne kawai muyi aiki''.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.