Isa ga babban shafi
Nijar

Kamfanin Cominak zai rufe nan da shekaru biyu masu zuwa

Kamfanin hako Uranium na Cominak a Arlit
Kamfanin hako Uranium na Cominak a Arlit AFP PHOTO PIERRE VERDY

Kasuwar Uranium da ta share tsawon shekaru tana fuskantar koma baya, a jamhuriyar Nijar daya daga cikin bangarori biyu na katafaren kamfanin samar da makamashin nukiliya na kasar Faransa Orano tsohon kamfanin Areva ba wata tantama zai rufe kofofinsa nan da shekaru biyu zuwa uku, sakamakon rashin kudi.

Talla

A makon da ya gabata ne a gaban yan majalisar dokokin kasar Nijar ministan ma’adinan karkashin kasar, Hassane Barazé ya bayyana mumunan sakamakon da kamfanin Cominak ya cimma, daya daga cikin mahakar ma’adinan mafi dadewa a kasar, da kasashen Faransa da kamfaninta na Orano, da japan da kamfaninta na Overseas Uranium sai kuma Spain da kamfaninta na ENU ke da hannun jari a ciki.

Wannan shekara da wasu shekaru biyu masu zuwa gibin kudin da kamfanin ke fuskanta zai kara zurfi . lisafin mai sauki ne, tare da kashe kimanin Euro 75 kafain samar da kilogram 1 na Uranium ya yi matukar tsada idan aka auna da yadda ake sayar da kilogram guda a kasuwar Duniya kan Euro 54 zuwa 55.

Duk da cewa a shekarar da ta gabata kamfanin Orano ya amince ya daga farashinsa , amma duk da haka bai wadatar ba.

Lura da cewa mahakar ta kawo karshen rayuwarta, sai an yi ta kara gina zuwa kasa da nisa kafin a cimma ma’adanin mai kyau.

Alamun dake nuna cewar kasuwar ta ji jiki,kasar jamhuriyar Nijer na ci gaba da janyo wasu sabin kamfanonin hakar ma'adinai, ta haka ne a watan yuli mai zuwa kasar Canada da kamfaninta na Goviex zata dora tubalin farko na kafa kamfanin sarrafa maádanai. Haka kuma domin kara janyo kamfanonin na waje gwamnatin ta Nijar ta yi kokari sosai wajen harajin da take karba, sai dai duk da haka a cewar kalaman minista Baraje kudaden da Uranium ke samarwa kasar na ci gaba da kankancewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.