Isa ga babban shafi
Sudan

An cimma yarjejeniyar kafa gwamnati a Sudan

Daya daga cikin masu zanga-zanga a Sudan rike da tutar kasar
Daya daga cikin masu zanga-zanga a Sudan rike da tutar kasar OZAN KOSE / AFP

Sojoji da kuma jagoran masu zanga-zangar neman sauyi a Sudan sun cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin riko wadda za ta share tsawon shekaru uku kafin shirya sabbin zabubuka a kasar.

Talla

Janar Yasser Atta, mamba a majalisar koli ta mulkin sojin kasar ne ya sanar da kulla wannan yarjejeniya bayan share tsawon kwanaki ana tattaunawa tsakanin bangarorin biyu.

A lokacin wannan tattaunawa, wasu sun bukaci amincewa da wa’adin shekaru 2 a matsayin na rikon kwarya, yayin da wasu suka bukaci shekaru 4, inda daga karshe aka amince da shekaru 3 a cewarsa.

Janar Atta ya ce, watanni shiddan farko za su kasance na tattaunawa ne domin samar da zaman lafiya da kungiyoyin ‘yan tawaye da ke yammaci da kuma kudancin kasar.

Hari ila yau yarjejeniyar ta amince da kafa majalisar dokoki ta rikon kwarya mai kujeru 300, kuma kashi 2 cikin uku na wakilan majalisar za su kasance wakilan masu zanga-zanga, yayin da sauran za su fito daga jam’iyyun siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.