Isa ga babban shafi
Afrika

Ana cin zarafin masu auren jinsi a Kamaru

Kungiyar masu auren jinsi a kasar Taiwan
Kungiyar masu auren jinsi a kasar Taiwan REUTERS/Tyrone Siu

A kasar Kamaru, masu auren jinsi sun yi zargin cewa ana cin zarafinsu tare da hana su samun kulawa a fannin kiwon lafiya, lamarin da ke zama daya daga cikin dalilan da ke kawo cikas a kokarin yaki da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV ko kuma Sida,

Talla

A cewar kungiyar Coalition Plus akalla masu auren jinsi dubu daya da 134 ne aka ci wa zarafi cikin shekarar da ta gabata a kasar, kamar dai yadda shugaban kungiyar Yves Yomb ke cewa.

Abin da mamaki gaskiya irin halayen da jami’an kiwon lafiya ke takawa don hana jama’a kamuwa da cutar HIV, musamman ma wariyar da ake nuna wa masu auren jinsi.

Ba shi kenan ba, domin kuwa shugaban kungiyar Yves Yomb ya karasa da cewa muna fuskantar wariya da kuma cin zarafi a cikin al’umma. An riga an kafa dokoki da ke bayar da damar hukunta wadannan mutane, saboda haka ba ta yadda za a yi nasarar shawo kan wannan cuta kafin shekara ta 2030

Irin wadannan mutane ba za su iya fitowa fili su bayyana kansu ba domin a yi masu gwaji, ana kama su sannan garkame su a gidajen yari, gaskiya suna bukatar samun ‘yanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.