Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Boko Haram ta kashe wasu karin Sojin Najeriya a Borno

Wasu dakarun sojin Najeriya
Wasu dakarun sojin Najeriya Reuters

Rahotanni daga Najeriya sun ce mayakan boko haram sun kashe sojojin kasar guda 3 a wani farmaki da suka kai sansanin sojin su da ke Jihar Barno mai fama da hare-haren ta'addanci.

Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito majiyar sojin na cewa, mayakan sun kai harin ne da misalign karfe 7 na yammacin jiya, abinda ya kai ga musayar wuta tsakanin bangarorin biyu.

Rahotanni sun ce daukin da sojojin suka samu ya ba su galabar kashe maharan da kuma tilasta musu tserewa, sai dai su kuma sun rasa sojinsu 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.