Isa ga babban shafi
Najeriya-Zamfara

Kotun Koli ta yi watsi da zababbun wakilan APC a Zamfara

Tambari ko alamar kotunan Najeriya
Tambari ko alamar kotunan Najeriya The Guardian

Kotun kolin Najeriya ta yi watsi da 'Yan takarar Gwamna da 'yan Majalisun Tarayya da na Jihar Zamfara da Jam’iyyar APC ta gabatar a zaben da akayi wannan shekara saboda zargin cewar Jam’iyyar ba ta gudanar da zaben fidda gwani ba kamar yadda hukumar zabe ta gindaya.

Talla

Alkalan kotun kolin guda 5 suka yanke hukuncin yau juma’a, abinda ya kawo karshen takaddamar da aka kwashe dogon lokaci ana yi tsakanin Jam’iyyar APC da sauran Jam’iyyun da suka shiga zaben.

Alkalan kotun sun ce 'yan takarar Jam’iyyun da suka zo na biyu a zaben da akayi, su ne za su hau kujerun da 'yan takarar Jam’iyyar APC suka lashe.

Alkalan sun ce ba bu yadda za’ayi Jam’iyyar da ba ta da halartattun 'yan takara ta shiga zabe.

Wannan hukunci ya nuna cewar jam’iyyar PDP ce za ta karbe kujerar Gwamna da na 'yan Majalisun saboda ita ta zo ta biyu a zaben da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.