Isa ga babban shafi
Kamaru

Mayakan Boko Haram sun hallaka mutane 26 a arewacin Kamaru

Wasu dakarun sojin kasar Kamaru.
Wasu dakarun sojin kasar Kamaru. REUTERS/Joe Penney

Jami’an tsaro a kasar Kamaru sun sanar da cewa mayakan kungiyar BokoHaram sun kashe mutane 26 a harin da suka kai Yankin Arewacin kasar a daren ranar lahadi.

Talla

Wata majiyar soji tace sojoji 17 da fararen hula 9 aka kashe sakamakon fafatawar da jami’an tsaro suka yi da mayakan a Darak, wani tsibiri dake kusa da tafkin Chadi.

Majiyar sojin tace an kama mayakan 40, yayin da sojoji 7 suka bata.

Wannan shi ne hari mafi muni da mayakan suka kai a cikin ‘yan watanni da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.