Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya dau alkawali na kawo gyara da ya dace a Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a dandalin Eagle Square dake Abuja
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a dandalin Eagle Square dake Abuja Ng.gov.jpg

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhar a yau 12 ga watan yuni ya kira yan kasar da su dafa ma sa a wannan sabuwar tafiya,ya kuma yi alkawali kawo gyara ga rayuwar yan kasar a lokacin da ake gudanar da bikin ranar demokradiya a Abuja.

Talla

Shugabanin kasashen Nijar,Gambia,Chadi da wasu manyan baki daga kasashe aminan Najeriya ne suka halarci bikin na Abuja.

Yan Najeriya da dama ne yanzu ke sa ran gani Shugaba Buhari ya aiwatar da manyan sauye-sauye kamar dai yada ya dau alkawali a lokacin yakin zabe.

Shugaba Buhari ya sanar da canza ranar 29 ga watan Mayu a matsayin ranar rantsar da sabbin Shugabani,yayinda ranar 12 ga watan Yuni zata kasance  ranar demokradiya.

Shugaban Najeriya ya baiwa filin wasa na Abuja sunan MKO Abiola.

Wani abin lura shine ta yada tsoffin Shugabanin Najeriya da suka hada da Goodluck Johnatan,Olusegun Obasanjo suka kauracewa bikin na yau.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.