Isa ga babban shafi
Afrika

Yan tawayen Janjaweed sun kashe mutane 9 a Darfour

Yankin Darfu a cikin Sudan
Yankin Darfu a cikin Sudan Reuters/路透社

Kungiyar yan tawayen Darfur da ake kira Janjaweed ta kashe mazauna wani kauye su 9 a yankin Darfur.Kwamitin likitocin dake shirya zanga zanga a kasar yace an kashe mutanen ne a ranar litinin da ta gabata, a kauyen Al Dalij dake Tsakiyar Darfur.

Talla

Hukumomin Sudan sun sanya yayan kungiyar Janjaweed da tayi kaurin suna wajen cin zarafin Bil Adama cikin rundunar dake taimakawa jami’an tsaro a Yankin.

A baya dai Dakarun Majalisar Dinkin Dinkin Duniya dake aikin wanzar da zaman lafiya a yankin Darfur dake kasar ta Sudan sun bayyana damuwar su kan sabon tashin hankalin da aka samu tsakanin kungiyoyi da masu ruwa da tsaki a harakar tsaron kasar ta Sudan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.