Isa ga babban shafi
Benin

Tashin hankali ya barke a garuruwan Savè da Tchaourou

Wasu jami'an tsaron Jamhuriyar Benin yayin sintiri a birnin Cotonou.
Wasu jami'an tsaron Jamhuriyar Benin yayin sintiri a birnin Cotonou. AFP / Yanick Folly

Al’ummar garuruwan Save da Tchaourou a wannan Juma’a sun tsinci kansu cikin zaman zulumi, bayan da lamura suka ci gaba da yamutsewa a wasu yankunan biranen da ke Jamhuriyar Benin, bayan shafe kwanaki ana gwabza fada tsakanin 'yan tauri magoya bayan tsohon Shugaban kasar Boni Yayi da kuma jami'an tsaro.

Talla

Rikicin dai ya samo asali ne daga yadda magoya bayan tsohon shugaban kasar Boni Yayi suka yi kokarin tilastawa jami'an tsaro janye daurin talalar da ake yiwa tsohon shugaban.

Rahotanni daga birnin Cotonou cibiyar hada-hadar kasuwanci ta kasar sun ce, an tura dubban sojoji zuwa yankunan da rikicin ya barke, inda aka bayyana cewa sojoji sun bude wuta kan farraren hula.

Lamarin dai ya kai ga haifar da kazamar arrangama tsakanin sojojin da wasu gungun mutane, har ta kai ga tilasatawa wasudaga cikin jami’an tsaron tserewa.

A halin da ake ciki yanzu haka yan kasar ta Jamhuriyar Benin da dama ne suka wayi garin cikin zulumi kasancewar wannan shi ne karo na farko da kasar ta taba fadawa cikin yanayi na yaki tsakanin dakarun kasar da mutanen wani yanki.

Garuruwan Save da Tchaourou, na daga cikin yankunan da motocin sufuri kama daga Nijar, zuwa Burkina Faso ke amfani da su, don safarar kayayyaki zuwa ciki da wajen Benin.

Rikicin na da ya kuno kai kuma ya dakatar da komai a cewar, Lawal Iro wani mai kula da fiton kayayyaki, da motar sa ke gaf da shiga garin na Tchaourou.

Wasu dattijan kasar, ‘yan kasuwa da sauran masu fada a ji, sun bukaci gaggauta yin sulhu tsakanin masu ruwa da tsaki ta fuskar siyasa, tareda fatan shugaban kasar ta Benin zai saurari koken al’umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.