Isa ga babban shafi
Habasa-Amurka

Ethiopians Airlines ya wanke matukinsa kan sakaci a hadarin Maris

Jirgin Kamfanin Ehiopian Airlines samfurin Boeing 737 kirar Amurka
Jirgin Kamfanin Ehiopian Airlines samfurin Boeing 737 kirar Amurka REUTERS/Amr Abdallah Dalsh

Kamfanin jiragen sama na Ethiopian Airlines a Habasha ya ki amincewa da rahoton wani binciken kwararru da Amurka ta gudanar kan musabbabin hadarin jirgin Boeing 737 wanda ya nuna matukan jirgin kamfanin ne ke da laifin haddasa faruwarsa.

Talla

A cewar shugaban kamfanin na Ethiopian Airlines, Tewolde GabreMariam yayin wata tattaunawa da shi a yau Litinin, babu adalci a yadda ake ci gaba da caccakar matukin jirgin na su, bayan kuma kowa na da masaniyar cewa samfurin jirgin na Boeing MAX 737 ne ke da matsala ba wai kamfanin su.

Mr Gabrelmariam ya bayyana cewa hatta majalisar Amurkan ba ta da wata hujja a hannu da ke nuna cewa matukin kamfanin ne ke da matsala ko kuma shi ne ya yi sanadiyyar afkuwar hadarin na watan Maris da ya hallaka mutane 157.

A watan da ya gabata ne dai wani dan majalisar Amurka na Jam’iyyar Republican Sam Graves yayin jawabin da ya gabatar gaban zaman majalisar ya yi kakkausar suka ga matukin jirgin na Ethiopian Airlines yana mai cewa shi ya haddasa hadarin sandiyyar wasu kura-kurai da ya aikata, duk kuwa da cewa ya samu cikakken horon tukin jirgin a Amurka.

Dan majalisan na Amurka ya ce bincikensu ya nuna cewa matukin jirgin ya samu cikakkiyar kwarewa kan yadda zai tunkari matsala makamanciyar wadda ta haddasa hadarin jirgin amma ya gaza yin kokari wajen shawo kan matsalar.

Sai dai cikin martinin Mr Gabremariam gad an majalisa Graves, ya ce ko kadan matukin jirgin na sub a shi da matsala tangarda daga samfurin jirgin wand aba wannan ne karon farko da ya fara yin hadari ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.