Isa ga babban shafi
Masar

Tsohon shugaban Masar Mohammed Morsi ya mutu a gaban Kotu

Tsohon shugaban kasar Masar Mohammed Morsi
Tsohon shugaban kasar Masar Mohammed Morsi DR

Rahotanni daga kasar Masar sun ce tsohon Shugaban kasar Masar, Mohammed Morsi ya mutu yau a gaban Kotu lokacin da ake tsaka yi masa shari'a bayan shafe tsawon lokaci daure a kurkuku.

Talla

Kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito kafofin yada labaran Masar na cewa Morsi ya yanke jiki ya fadi ne a kotu inda aka ruga da shi asibiti, ya kuma ce ga garin ku nan.

Shugaba AbdelFatah al Sisi ya yiwa Morsi juyin mulki ya kuma daure shi a gidan yari.

Tsohon shugaban shi ne zababen shugaban Masar na farko, amma kuma bayan shekara guda sojoji suka kawar da shi a karagar mulki a watan Yulin shekarar 2013.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.