Isa ga babban shafi
Nijar

An yi nasarar kawo karshen zanga-zanga a jihar Maradi ta Nijar

Kofar shiga garin Maradi cibiyar kasuwancin Jamhuriyar Nijar
Kofar shiga garin Maradi cibiyar kasuwancin Jamhuriyar Nijar PIUS UTOMI EKPEI / AFP

Al’amura sun dai-dai ta a garin Maradi cibiyar kasuwancin jamhuriyar Nijar, bayan da aka samu hatsaniya a birnin sakamakon zanga-zangar da ta biyo bayan kama wani hamshakin malamin addinin Islama a yankin.

Talla

Gwamnan jihar Maradi Zakary Oumaru, a zantawarsa da manema labarai ya ce, kura ta lafa yanzu a birnin bayan da malamin addinin Sheik Raydoune Issaka, ya amice da aikata laifi ya kuma bada hakuri, kazalika kungiyar malamai ta kasa itama da bada hakuri da cewar hakan bazai kara aukuwa ba.

Matakin kame malamin Sheik Raydoune Isaka, na babbar masallacin Sahaba da ke anguwar Zarian Maradi, ya biyo bayan wata hudubar sallar juma'a da ya yi wadda ta  kalubalanci wata doka da gwamnati ke son majalisa ta amince da ita, inda Limamin ya bayyana dokar a matsayin wadda ta yi hannun riga da koyarwar addinin islama.

Tun daga daren Asabar 15 ga watan Yunin 2019 ne dubban jama'a suka tsunduma zanga-zanga da matakin kame malamin wadda ta kai ga kone-konen makarantu, motoci, da kuma mujami'u, abin da hukumomi suka danganta da cewar bata gari sunyi amfani da damar wajen fasa shaguna da kuma satan dukiyoyin al’umma, abin da ya kai ga kama mutane 178, wanda yanzu haka ke tsare kuma ana gudanar da bincike akansu.

Tuni kungiyar malaman yankin ta fito ta nuna alhininta kan wannan lamari da ya haifar da barnata dukiyar al’umma a garin maradi cibiyar kasuwancin kasar, kakakin kungiyar Imam Hafizou Samaila Maradawa, ya ce ba da yuwunsu aka gudanar da zanga-zangar ba.

Yanzu haka dai masu ruwa da tsaki a yankin da kungiyar malamai ta jihar da ma sauran mukarraban gwamnti bisa jagorancin gwamnan Maradi Zakary Oumaru, sun kai ziyar gani da ido wurare da aka barnata cikin harda mujami’ar da aka kone kurmus, lamarin da ya sa Sheik Issaka, zubda hawaye tare da neman gafarar shugabancin majami'ar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.