Isa ga babban shafi
Najeriya-CHAD

An fafata tsakanin dakarun Chadi da yan Boko Haram

Dakarun Chadi
Dakarun Chadi © Thomas SAMSON/Gamma-Rapho via Getty Images

Sojojin Chadi 10 ne suka rasa rayukan a wani gumurzu da ya hada dakarun kasar da mayakan Boko Haram a garin Fodio dake daf da tafkin Chadi da Najeriya.

Talla

Tsawon wata daya baya kenan da akalla sojojin Chadi hudu da na Najeriya uku sun rasa rayukansu a wasu mabanbantan hare-haren da kungiyar Boko Haram ta kai.

Sojin Najeriya kuwa sun rasa rayukansu ne a harin da kungiyar ta kai musu a sansanin garin Gubio mai tazarar kilomita 80 daga babban birnin Maiduguri na jihar Borno.

Maharan sun kai farmakin ne da yammacin jiya Asabar, inda suka yi lugudan wuta tare da fatattakar sojojin na Najeriya.

A wata yarjejeniya dake tsakanin kasashen yankin Sojojin kasashen da suka hada da Nijar ,Cadi, Najeriya za su iya shiga kasashen juna domin yakar yan ta’ada.

Wata majiya da shwalkwatar sojan Cadi na nuni cewa fadan tsakanin sojojin Cadi da mayakan Boko Haram a jiya ya fi muni,wanda ya kai yan kungiyar ta Boko Haram janyewa daga wannan shige na Fodio da suka kafa tareda barin gawawakin mutane 23.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.