Isa ga babban shafi

Sojin Habasha sun hallaka jagoran juyin mulkin kasar da bai yi nasara ba

Firaministan Habasha Abiy Ahmed bayan yunkurin juyin mulkin kasar da bai yi nasara ba
Firaministan Habasha Abiy Ahmed bayan yunkurin juyin mulkin kasar da bai yi nasara ba HO / Ethiopian TV / AFP

Gwamnatin kasar Habasha ta tabbatar da kashe mutumin da ake zargi da kitsa yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba, a Yankin Amhara, bayan kashe babban hafsan sojin kasar da kuma shugaban Yankin.

Talla

Ofishin Firaminista Abiy Ahmed ya bayyana mutumin a matsayin Asaminew Tsige wanda aka taba daurewa da irin wannan yunkuri kafin Firaminista Ahmed ya sake shi a karkashin shirin sa na yiwa jama’a afuwa.

Tashar talabijin din Habasha ta ce an kashe Tsige ne a inda ya ke buya da ke birnin Bahir Dar na kasar.

Rahotanni sun ce kafin kisan na karshen mako, Tsige ya bayyana a kafar facebook inda ya ke bukatar 'yan kasar su tanadi makamai domin kai hare-hare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.