Isa ga babban shafi
Habasha

Jami'an tsaro a Habasha, sun kama mutane 56 da laifin kabilanci

Firayi ministan Etciopia  Abiy Ahmed
Firayi ministan Etciopia Abiy Ahmed HO / Ethiopian TV / AFP

Jami’an tsaro a Habasha, sun cafke mutane 56, dukkaninsu magoya bayan jam’iyyar masu tsatsauran ra’ayi da kabilanci a lardin Amhara, bisa zarginsu da hannu da yunkurin juyin mulkin da aka yi cikin makon jiya a lardin.

Talla

Mai magana da yawun jam’iyyar National Amhara Movement Mr Christian Tadele, ya ce a Adis Ababa kawai an cafke magoya bayan jam’iyyar su 56 yayin da aka kama wani adadi mai tarin yawa a lardin Oromo.

Tadele, ya ce kamen ba wai ya dogara ba ne kan dalilain siyasa kawai ba, wani lokaci ana kama mutane ne saboda kasancewarsu ‘yan kabilar Amhara, abin da ke nufin cewa, ana kafa hujja da kabilanci ne domin kama jama’a.

A ranar asabar da ta gabata ne, aka kashe manyan jami’an gwamnatin lardin Amhara su uku, da suka hada da shugaban lardin da kuma babban kwamandan askarawan kasar Janar Seare Mekonnen a wani abu da aka bayyana cewa yunkurin juyin mulki ne.

Masana siyasar kasar ta Habasha, na danganta wannan yunkuri na juyin mulki a matsayin adawa da wasu daga cikin sauye-sauyen da Firaministan kasar Abiy Ahmed ke kan aiwatarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.