Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Farfesa Shehu Abdullahi Zuru kan yadda al'ummar Anambra ta yiwa Fulani makiyaya korar kare

Sauti 03:40
Wasu makiyaya a sassan Najeriya
Wasu makiyaya a sassan Najeriya STEFAN HEUNIS/AFP/Getty Images

Rahotanni daga Jihar Anambra a Najeriya na nuna cewar wasu mutanen garin sun kori Fulani makiyaya da ke kiwon shanu a garin Nnewi, matakin da ya haifar da mahawara mai zafi a kafofin sada zumunta. Hotan bidiyon da aka nada aka kuma wallafa shi a intanet ya nuna yadda mutanen garin dauke da sanduna da adda suka sanya makiyaya a gaba suna korar su, yayin da hukumomi suka yi gum.Domin sanin hadarin da ke tattare da daukar irin wannan mataki da kuma barazanar da ke tattare da shi, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin shari’a Farfesa Shehu Abdullahi Zuru na Jami’ar Abuja, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.